Kalaman na Mr. Geng na zuwa ne bayan da a kwanakin baya, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson, ya bayyana cewa kasar ba ta nemi hanyar sauya gwamnatin kasar Koriya ta Arewa, ko yunkurin hambarar da gwamnatin kasar, ko hanzarta neman hanyar dinke Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa wuri guda. Kaza lika ba ta nemi wata hujja, ta shiga Koriya ta Arewa. A maimakon hakan, Amurka na fatan Koriya ta Arewa za ta fahimci cewa, ba za ta iya samun tsaro da ci gaba ba, har sai an kawar da makaman nukiliya daga zirin Koriya. (Tasallah Yuan)