in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fadar White House: kasar Sin ba ta sarrafa darajar kudin musaya ba
2017-04-18 13:48:15 cri
Kakakin fadar White House ta kasar Amurka Sean Spicer, ya jaddada cewa, kasar Sin ba ta sarrafa darajar kudin musayar ta ba, tun bayan shugaban kasar Donal Trump ya kama aikinsa.

Mista Spicer ya bayyana hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyi, a gun taron manama labaru da aka saba shiryawa a fadar ta White House a jiya Litinin, inda ya kara da cewa, dalilin da ya sa ma'aikatar kudin kasar Amurka ba ta zargi Sin da sarrafa darajar kudin na ta ba shi ne, ba wasu shaidu na zahiri dake tabbatar da hakan.

A kwanan baya, shi ma shugaban Amurka Donald Trump, yayin zantawar sa da jaridar wall street journal, ya tabbatar da cewa, Sin ba kasa ce dake sarrafa darajar kudin musayar ta ba, wanda hakan ke nuna cewa ya sauya matsayin sa kan wannan batu, sabanin irin kalaman da ya rika furtawa, lokacin da yake yakin neman zaben sa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China