Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Robert Hormats ya yi hasashen cewa, ta wannan ganawa, shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, da manyan batutuwan kasa da kasa da yankuna, da tsaida hanyar bunkasa dangantakar dake tsakaninsu a sabon lokaci, kana sun kafa kyakkyawar hulda a tsakanin shugabannin biyu.
Shugaban ofishin nazarin harkokin gabashin kasashen duniya na kwalejin tattalin arziki ta kasar Rasha Alexei Maslov ya bayyana cewa, wannan ganawa za ta bude sabon shafi ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Shugabannin kasashen biyu sun shaida matsayinsu na son yin shawarwari da juna, wannan kyakkyawan tushe ne na neman samun daidaito ta hanyar yin mu'amala.
Masani kan harkokin kasashen waje na Jami'ar Nairobi ta kasar Kenya Patrick Maluki, ya bayyana cewa shugabannin biyu dukkansu sun bayyana wannan ganawa tana da babbar ma'ana da kyakkyawan sakamako, kana sun amince da yin kokari tare don fadada hadin gwiwarsu da samun moriyar juna, ta haka za a sa kaimi ga bunkasar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)