Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yau Laraba cewa, yayin da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson ya kawo ziyara nan kasar Sin, kasashen biyu sun cimma daidaito kan raya dangantakar dake tsakaninsu, bisa tunanin watsi da adawa, da girmama juna, da hada kai domin moriyar juna. Sin da Amurka sun amince wadannan hanyoyi su ne mafiya dacewa wajen raya dangantakarsu yadda ya kamata.
Hua Chunying ta bayyana cewa, Sin na fatan kara mu'amala tare da Amurka, a fannin kara fahimtar juna, da imani da juna, da warware matsalolinsu yadda ya kamata, da fadada hadin gwiwarsu a matsayi na kasa da kasa da ma na yankuna. Ta ce ta haka ne za a kai ga daukaka dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)