in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta musanta ikirarin jami'in Birtaniya da ya zarge ta da kisan kare dangi
2017-04-15 12:04:56 cri

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta musanta cewa ana kisan kiyashi a kasar. Wannan ya biyo bayan tsokaci da Sakataren Birtaniya kan shirin raya kasashe Priti Patel ya yi a ranar Laraba da ta gabata, inda ya ce ana kisan kare dangi a kasar dake fama da rikici.

Kakakin Shugaban kasar Salva Kiir, Ateny Wek Ateny, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, babu yadda za a yi gwamnati ta rika yi wa al'ummarta kisan kare dangi, yana mai karyata wadanda suka yi wannan ikirari.

Ana zargin dakarun gwamnati da farwa fararen hula a garin Yei na kudu maso yammacin kasar dake fama da rikici.

Kuma a cikin bara ne bayan ziyartar garin dake kan iyaka, mashawarci na musammam na MDD kan kare aukuwar kisan kare dangi, Adama Dieng, ya ce akwai yiyuwar aukuwar kisan a garin.

Kakakin na Shugaban kasar, ya kuma musanta ikirarin da jami'in na Birtaniya ya yi, inda ya ce akwai bukatar kasashen Afrika su tsoma baki, domin yayyafawa rikicin kasar ruwan sanyi maimakon nade hannu suna jiran taimakon kasashen waje. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China