in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 3 sun rasu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai kudancin Somaliya
2017-05-13 13:40:47 cri
Wani jami'in gwamnatin kasar Somaliya ya bayyana ewa, an kai harin kunar bakin wake a kudancin kasar a jiya da yamma, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla guda 3, cikin hada da maharin.

Kakakin ma'aikatar harkokin tsaron Somaliya Ahmed Arab, ya bayyanawa manema labarai a kasar cewa, an kai harin kunar bakin waken wanda ake zargin kungiyar Al-Shabaab da kaiwa, a garin Kismayo dake kudancin kasar.

Ban da maharin, 'yan mata biyu ne suka mutu sanadiyyar harin, inda wani mutum guda ya jikkata.

Ahmed Arab ya kara da cewa, rundunar sojojin za ta dauki matakan riga kafi kan hare-haren da mai yuwa za a iya kai wa a nan gaba, sannan za ta hada gwiwa da tawagar musamman da kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta tura zuwa kasar domin yaki da mayakan Al-Shabaab.

Kungiyar Al-Shabaab, kungiya ce mai tsattsauran ra'ayi dake mubaya'a da kungiyar AL-Qaeda, kuma a shekarun baya bayan nan, ta yi ta kai hare-haren ta'addanci kasar Somaliya da wasu kasashen kewayenta.

Haka kuma, rundunar sojojin kiyaye tsaro ta kasar Somaliya ta hada gwiwa da rundunar sojin kungiyar AU, da nufin daukar matakan soji da dama da za su murkushe kungiyar ta Al-Shabaab gaba daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China