in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mika mutane 3 da ake zarginsu da yin fashi a teku ga mahukuntan Puntland na Somaliya
2017-05-11 20:12:37 cri

A ranar Alhamis din nan ne hukuma mai kula da harkokin watsa labaru, ta ma'aikatar tsaron kasar Sin ta tabbatar da cewa, a ranar 5 ga wata bisa agogon wurin, kasar Sin ta mika wasu mutane 3 da ake zarginsu da yin fashi a teku ga mahukuntan Puntland na kasar Somaliya, bayan da sojojin Sin suka cafke su a yayin da suke ba da kariya ga jirage masu zirga-zirga a teku.

hukumar ta ma'aikatar tsaron kasar Sin ta kuma jaddada cewa, rundunar mayakan ruwan kasar Sin, za ta ci gaba da tura jiragen ruwan soja domin ba da kariya ga jiragen dake zirga-zirga a teku. Kaza lika Sin za ta ci gaba da sauke nauyin dake kan ta a duniya, a mataki na kara taka rawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya, da kuma tabbatar tsaron hanyar sufuri ta kasa da kasa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China