in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR ta dawo da 'yan gudun hijirar Somaliya kimanin 62,000 daga Kenya
2017-04-25 20:35:24 cri
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR ta bayyana a yau Talata ce tun lokacin da ta fara shirin mayar da 'yan gudun hijirar Somaliya daga Kenya a watan Disamban shekarar 2014 zuwa yanzu, ta kwashe kimanin 'yan gudun hijirar kasar ta Somaliya 61,665 daga kasar ta Kenya zuwa gida.

Bayanai na nuna cewa, akwai sama da 'yan Somaliya miliyan biyu da aka raba da muhallansu a kasar da ta shiga shekarunta na 30 tana fama da matsalar harkokin jin kai a duniya.

Kwararru na cewa, rikicin siyasa da matsalar tsaro da kasar Somaliya take fuskanta, gami da matsin lamba daga kasashen da 'yan kasar ta Somaliya ke gudun hijira a cikinsu, sun kara dagula kokarin da ake na magance matsalar 'yan gudun hijirar kasar ta Somaliya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China