in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da samar da Karin kudade don kawar da yunwa a Somalia
2017-05-11 10:26:27 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kara ayyukan jin kai da kudade da za su taimaka wajen kawar da matsananciyar yunwa a Somalia.

Cikin wata sanarwar da aka fitar a jajibirin ranar da za a yi taro kan Somalia a birnin London, Guterres ya yi kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe da gwamnatin Somalia da kuma hukumomi masu bada agajin jin kai domin magance matsalar ta yunwa.

Kasar dake kahon Afrika, na fama da matsalar fari da ya jefa mutane miliyan 6.7, adadin da ya kai rabin al'ummar kasar, cikin bukatar agajin jin kai.

Sakatare Janar MDD da shugaban kasar Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed, za su gabatar da wani shiri kan agajin jin kai don kawar da yunwa a kasar ga al'ummomin kasashen duniya, yayin taron da zai gudana yau Alhamis a birnin London.

Shirin wanda aka sake yi wa bita, na bukatar dala biliyan 1.5 domin kai wa mutane miliyan 5.5 dauki a bana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China