in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kori 'yan kasashen Somaliya da Kenya guda 72
2017-05-13 13:36:38 cri
Rundunar 'yan sandan Kenya da hukumar kula da shige da fice ta kasar, a jiya Jumma'a, sun tabbatar da cewa, Amurka ta kori 'yan kasar Somaliya 67 da 'yan Kasar guda 5.

Haka zalika, wani jami'in gwamnatin kasar da bai fadi sunansa ba, ya bayyana wa manema labarai cewa, Amurka ta kori mutanen 72 ne saboda matsalar karancin takardun shaidar zama da sauran wasu abubuwa masu alaka da wannan, inda ya ce tuni mutanen suka isa birnin Nairobi a jiya da safe, sannan, su ma 'yan kasar Somaliya guda 67 za su tafi Mogadishu, babban birnin kasar.

A yayin babban zaben shugaban kasar Amurka da aka yi a shekarar da ta gabata, Donald Trump ya yi alkawarin cewa, bayan ya rike ragamar mulkin kasar, zai hana shigar 'yan cin rani ba bisa ka'ida ba, yayin da kara mai da hankali ga 'yan cin rani da suka riga suka shiga kasar ba bisa doka ba.

Kuma bayan ya kama aiki a matsayin shugaban kasar Amurka ne, har sau biyu, ya ba da umurni a hukumance na hana wasu 'yan kasashen ketare shiga Amurka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China