Sanarwar da 'yan sandan kasar suka bayar ta nuna cewa, wata mota mai dauke da boma-bomai ta kutsa kai cikin wani wurin cin abincin irin na Italiya, sa'an nan ta fashe, al'amarin da ya haddasa mutuwar mutane 5, tare da raunata wasu 10.
Ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu, la'akari da raunuka masu tsanani da wasu mutane suka samu.
Kungiyar Al-Shabab ta masu tsattsauran ra'ayi, wadda ke da alaka da kungiyar ta'addanci ta Al-Qaeda, ta sanar da daukar alhakin wannan hari.(Bello Wang)