A rahotonsa na baya-bayan nan, ofishin kula da harkokin bada agajin jin kai na MDD, ya ce cutar ta barke ne a yankuna 13 daga cikin 18 dake kasar Somalia.
Ya kuma alakanta barkewar cutar da matsalar karancin ruwa da abinci da gudun hijira, da ya jefa tabbatar da tsafta cikin wani hali.
Hukumar ta ce kusan mutane 32,000 ne suka yi fama da cutar, inda kuma 618 suka mutu tun daga farkon shekarar 2017.
Ta ce yara da manya dake kokarin rayuwa cikin matsalar rashin abinci da sinadarai masu gini jiki, wanda fari a bara ya haifar, su ne suka kamu da cutar sanadiyyar shan ruwa mara tsafta. (Fa'iza Mustapha)