Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Talata 28 ga wata a nan birnin Beijing cewa, Sin na maraba da kamfanonin kasa da kasa, su zuba jari tare da gudanar da ayyuka a kasar Sin, bisa girmamawa, da tabbatar da halastacciyar moriyarsu a cikin kasar. Ya ce tilas ne kamfanoni su gudanar da ayyukansu bisa dokoki, da ka'idoji a kasar Sin.
Kalaman na Mr. Geng dai na zuwa ne bayan da kamfanin Lotte, da ma'aikatar harkokin tsaron kasar Koriya ta Kudu, suka daddale yarjejeniyar mika wani yanki, domin a yi amfani da shi wajen jibge na'urorin THAAD na tsaro, lamarin da ya sanya jama'ar kasar Sin da dama ke nuna adawar su da kamfanin na Lotte.
Game da wannan batu, Geng Shuang ya bayyana cewa, Sin ta ki amincewa da matakin jibge tsarin THADD a kasar Koriya ta Kudu, kana za ta dauki matakai don tabbatar da moriyarta a fannin kiyaye tsaro. Kaza lika Sin ta kalubalanci bangarorin da abin ya shafa, da su maida hankali kan muradun kasar Sin, su kuma dakatar da ayyukan jibge na'urorin THADD, tare da kau da matakan tada zaune tsaye. (Zainab)