in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana damuwa game da atisayen soji dake gudana a zirin Koriya
2017-03-03 19:27:02 cri

Mahukuntan kasar Sin sun bayyana damuwar su, game da atisayen dakarun soji na hadin gwiwa, wanda Amurka da Koriya ta kudu suka fara a zirin Korea.

Da yake sake jaddada matsayar kasar Sin game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce kasar sa na matukar adawa da daukar duk wasu matakai na wuce iyaka, da suka hada da girke jiragen ruwan yakin Amurka a wannan ziri. Mr. Geng ya ce batun yankin zirin Korea na da sarkakiya da kuma jan hankali, don haka kamata ya yi, a maida hankali ga daukar matakan da zasu kwantar da hankula, da samar da daidaito a zirin, da ma daukacin yankin arewa maso gabashin nahiyar Asiya baki daya.

Daga nan sai ya nanata adawar da kasar Sin ke yi, da shirin girke na'urorin tsaron makamai samfurin THAAD, wanda Amurka da Koriya ta kudu ke baiwa goyon baya.

Rahotanni dai na cewa, dakarun hadin gwiwa dake atisayen soji a zirin na Koriya, za su ci gaba da wannan aiki ne har zuwa karshen watan Afrilun dake tafe.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China