Jawabin na mista Guterres ya zo ne, bayan wasu kalamai da shugaban Amurka Donald Trump ya yi a birnin Washington, a lokacin taron manema labarai tare da firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, inda ya ce shirin samar da kasashen biyu, ba shi kadai ne mafita ba, saboda irin rashin adalcin da MDDr take yiwa kasar Isra'ila.
Babban sakataren MDD ya jaddada kalaman nasa a wata lacca da ya gabatar, a jami'ar birnin Cairo, wadda ta samu halartar jami'an diplomasiyya da dalibai.
Guterres, ya bayyana rikici tsakanin Isra'ila da Palestinu, wanda aka shafe gwamman shekaru ana yi, a matsayin tushen rikicin shiyyar baki daya.
Ya ce dole ne a dauki kwararan matakai domin warware rikicin kasashen biyu da ya ki ci ya ki cinyewa, ya kara da cewa kasar Masar ita ce babbar jagora wajen warware duk wata takaddama da ta shafi yankin gabas ta tsakiya. (Ahmad)