in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shawarwari a tsakanin firaministocin Sin da Isra'ila
2017-03-21 10:36:26 cri

Jiya Litinin ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin.

A yayin shawarwarin, Li Keqiang ya jaddada cewa, a matsayinta na abokiyar kasashen Isra'ila da Palasdinu, kasar Sin tana fatan ganin Isra'ila da Palasdinu sun yi zauna tare cikin lumana, kana tana fata cewa, kasashen 2 za su ci gaba da bin "kafa kasar Palasdinu da ma ta Isra'ila tare", kuma su kai zuciya nesa, su maido da shawarwarin zaman lafiya cikin hanzari. Kasar Sin tana son ci gaba da tsayawa domin yin adalci, tare da yin kokari da kasashen duniya domin taka rawa mai yakini wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

A nasa bangaren, Benjamin Netanyahu ya ce, Isra'ila ta yi maraba da kamfanonin kasar Sin da su shiga ayyukan more rayuwar jama'a a Isra'ila, kuma tana son inganta hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2 ta fuskar sufuri da zirga-zirga. Har ila yau, Isra'ila ta yabawa kasar Sin dangane da kyakkyawar rawarta wajen shimfida zaman lafiya a yankin na Gabas ta Tsakiya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China