Wadannan kungiyoyin Falesdinawa 17, dukkansu suna cikin yankunan da dokar ta shafa, kuma sun gabatarwa kotun kolin Isra'ila takardar rokon ne bisa taimakon da kungiyoyin dokoki da kare hakkin dan Adam biyu na Isra'ila suka ba su.
Haka zalika, cikin sanarwar da kungiyoyin biyu suka bayar, an ce, dokar gina matsugunan Yahudawa da Isra'ila ta fitar, ta nuna amincewarta kan kwace yankuna mallakar Falesdinawa dake yammacin kogin Jordan, lamarin da ya keta ikon al'ummomin Falesdinu wadanda suke zaune a wuraren, wannan doka ta sabawa dokar kasa da kasa, ta kuma sabawa babbar doka ta Isra'ila.
A ranar 6 ga wata, majalisar dokokin kasar Isra'ila ta zartas da wani kudurin doka, wanda ya amince da matsugunan da wasu Yahudawa suka gina ko za'a gina a yankunan yammacin kogin Jordan ba tare da izni ba. (Maryam)