Kana, a yayin taron maneman labarai da aka yi a wannan rana a birnin Beirut na kasar Lebanon, Rima Khalaf, ta bayyana cewa, babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya bukace ta soke rahoton da ta fitar, amma ba ta son yin haka, shi ya sa, ta tsai da wannan kuduri na yin murabus.
Mr. Guterres ya karbi takardar yin murabus din da ta gabatar masa a yammacin ranar 17 ga wata.
A ranar 15 ga watan nan, kwamitin tattalin arziki da zamantakewar al'ummar yammacin Asiya ya fidda wani rahoto, inda ya zargi kasar Isra'ila da cewar, ta kafa tsarin mulki na nuna wariya tsakanin kalibu daban daban, domin yin mulki kan Falesdinawa.
Bugu da kari, malama Khalaf ta jaddada cewa, wannan shi ne karo na farko da MDD ta bayyana laifuffukan da Isra'ila take aikatawa kan alummar Falesdinu.
Kwamitin tattalin arziki da zaman takewar al'ummar yammacin Asiya shi ne rashen majalisar tattalin arziki da zaman takewar al'ummar MDD, kuma babban aikin kwamitin shi ne taimakawa kasashen dake yammacin nahiyar Asiya wajen raya tattalin arzikinsu. Rima Khalaf mai shekaru 64, wadda aka haife ta a kasar Jordan, ta hau kan matsayin babbar sakatariyar kwamitin tattalin arziki da zaman takewar al'ummar yammacin Asiya ne a shekarar 2010. (Maryam)