Shekaran jiya Litinin ne majalisar dokokin kasar Isra'ila ta zartas da wani shirin doka, wanda ya amince da matsugunan da wasu Yahudawa suka gina ko za'a gina a yankunan yammacin kogin Jordan ba tare da izni ba.
Shima a nasa bangaren, shugaban al'ummar Falasdinawa Mahmoud Abbas ya ce, wannan doka da majalisar dokokin Isra'ila ta amince da ita, ta keta dokokin kasa da kasa.
A wani labarin kuma, kasashen Jordan da Masar sun fitar da sanarwa a jiya Talata, inda suka yi tofin Allah tsine game da shirin dokar da Isra'ila ta amince da shi.(Murtala Zhang)