Kamfanin dillancin labaru na Mehr na kasar Iran ya ruwaito cewa, bangarorin uku sun tattauna kan batutuwan da suka hada da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Syria da musayar mutanen da aka yi garkuwa da su.
Ita ma tawagar masana ta MDD, ta halarci tattaunawar a matsayin mai sa ido.
A ranar 15 ga wannan wata ne, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, da takwaransa na Iran Mohammad Javad Zarif, da kuma na Syria Walid Muallem, suka gana a birnin Moscow na Rasha, inda suka tattauna kan harin da Amurka ta kai wa Syria, da yin bincike kan harin makamai masu guba da hanyoyin samar da zaman lafiya a Syria, da hada hannu wajen yaki da ta'addanci.
Bisa yadda aka tsara, za a gudanar da sabon zagayen taron shimfida zaman lafiya na Astana, a farkon watan Mayu. (Zainab)