in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara aiwatar da yarjejeniyar kafa yankin rage rikice-rikice a kasar Syria
2017-05-06 13:34:16 cri
Rahoton da jaridar Vatan gazetesi ta kasar Syria ta wallafa a shafinta na internet a yau Asabar ya ce an fara aiwatar da yarjejeniyar kafa tuddan mun tsira a kasar Syria.

A kwanakin baya ne, kasar Rasha ta gabatar da kafa tuddun mun tsira a jihar Idleb dake arewa maso yammacin kasar, da jihar Homs dake tsakiyar kasar, da kuma yankin karkara na Damascus, da yankin kudancin kasar, inda za a kafa tasoshin bincike a yankunan don magance aukuwar rikice-rikice.

Rasha, Turkiya da Iran sun zama kasashen dake goyon bayan kafa yankunan, kuma watakila za su tura sojoji don sa ido ga yanayin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yankunan

Baya ga haka, mayakan kungiyar masu tsattsauran ra'ayi za su dakatar da kai hare-hare yankunan.

Wakilan kasashen Rasha, Turkiya da Iran sun daddale yarjejeniyar kafa tuddan mun tsira a kasar Syria a birnin Astana dake kasar Kazakstan a ranar 4 ga wata.

Manyan jami'an kasar Rasha sun yi tsammanin cewa, kafa yankunan zai taimakawa gwamnatin kasar Syria da kungiyar masu adawa, tsagaita bude wuta ga juna da kaddamar da shawarwarin shimfida zaman lafiya a lokacin da ya dace. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China