in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya nada shugaban kwamitin da zai yi bincike kan amfani da makamai masu guba a Syria
2017-04-28 10:42:53 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Gutteres ya nada Edmond Mulet na kasar Guatemala, matsayin shugaban kwamitin da zai yi bincike kan amfani da makamai masu guba a Syria.

Wata sanarwa da MDD ta fitar jiya, ta ce Edmond Mulet shi zai shugabanci kwamitin mambobi 3 mai zaman kansa, da zai jagoranci wani bangare na hukumar haramta amfani da makamai masu guba wato hukumar hadaka ta MDD JIM, mai gudanar da bincike kan amfani da makamai masu guba a Syria, wanda kuduri na 2235 na kwamitin sulhu na majalisar ya kafa a shekarar 2015.

Sanawar ta ce a ranar 17 na watan Nuwamban bara ne kuduri na 2319 na kwamitin sulhun ya tsawaita wa'adin aikin hukumar JIM da shekara guda.

Sanarwar ta kuma ruwaito Sakatare Janar na MDD na jadadda kira ga dukkanin bangarorin Syria su bada goyon baya ga hukumar JIM, ya ce ya na mai dogara da tallafi da aikin mambobin kwamitin sulhu da sauran mambobin Majalisar wajen tabbatar da aiwatar da aikin JIM yadda ya kamata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China