Yang ya ce, kasar Sin ta ki yarda da duk wata aika-aikar yin amfani da makamai masu guba, kuma hanyar siyasa ce kadai ta fi dacewa wajen warware rikicin na Siriya. Kasar Sin na ganin cewa, ya kamata al'ummar Siriya su daidaita matsalar kasarsu, su ne za su yi zabi.
Sin da Turai sun cimma matsaya daya cewar, ya kamata a ci gaba da yin shawarwarin siyasa, da samar da tallafin jin-kai, da farfadowa gami da kare ababen more rayuwar al'umma a Siriyar, tare kuma da yaki da ayyukan ta'addanci, da kuma aiwatar da kudirorin kwamitin sulhun MDD yadda ya kamata.(Murtala Zhang)