Ma'aikatar harkokin kudi ta kasar Amurka, ta bayar da sanarwa a jiya Litinin, dake cewa za ta sanya takunkumi ga ma'aikata 271 na gwamnatin kasar Syria, masu nasaba da shirin kirkirar makaman kare dangi na gwamnatin kasar.
Sanarwar ta ce, wadannan ma'aikata 271 suna aiki ne a cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Syria, wadda ke kula da aikin kirkirar makaman kare dangi don gwamnatin kasar. Haka kuma sanarwar ta ce, a cikin wadanda aka sanyawa takunkumin daga dukkan fannoni, wasun su sun riga sun gudanar da irin wannan aiki ga gwamnatin Syria har na tsawon shekaru biyar.
Bugu da kari, sanarwar ta bayyana cewa, Amurka za ta haramta musu amfani da kadarorinsu da ke cikin kasar, kuma za ta hana kamfanoninta da jama'arta da su yi cinikayya da su.(Kande Gao)