A cikin wata sanarwar da ta bayar, tawagar MINUSMA ta yi Allah wadai da wannan hari, inda ta yi kira ga bangarori daban-daban da su gudanar da bincike don bankado madugun da ya jagoranci shirya makarkashiyar kai harin, ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da tallafawa kasar Mali gami da al'ummarta wajen farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali.(Murtala Zhang)