Kungiyar wadda ke da sansani a wasu yankunan arewacin nahiyar Afirka, ta bayyana cewa, sunan wanda ya kai harin Abdullah Hady, ko da yake ba ta yi wani karin haske game da shi ba.
A jiya Labara ne dai da karfe 8 da minti 40 na safe, aka kaddamar da harin bom da aka dana jikin wata mota, a sansanin sojin dake yankin Gao na arewacin kasar Mali, wanda nan take ya haddasa mutuwar mutane a kalla 50, tare da raunata mutane da dama.
An dai kafa sansanin da aka kaiwa harin ne don cimma yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a kasar Mali, kuma sojojin kasar Mali da dakarun dake goyon bayan gwamnatin kasar ne ke jibge sojojin su a sansanin. (Zainab)