in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rashin tashin rikici a kasar Mali ka iya kawo karshen matsalar gudun hijira zuwa karshen 2017
2017-03-04 12:06:12 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta duniya IOM, ta yi kiyasin cewa, idan har ba a samu sake barkewar rikici a kasar Mali ba cikin watanni masu zuwa, to za a iya shawo kan matsalar 'yan gudun hijira zuwa karshen shekarar nan.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban ofishin hukumar a kasar Mali Bakary Doumbia, ya ce idan har ba a sake samun barkewar rikici da zai daidaita mutane har ya kai su ga neman agajin jin kai ba, yana da yakinin cewa, zuwa karshen shekarar 2017 matsalar ta 'yan gudun hijira a kasar za ta zama tarihi.

Ya kara da cewa, a yanzu haka, adadin 'yan gudun hijirar ya ragu da sama da kashi 90 cikin 100.

Rahoton hukumar ta IOM ya bayyana cewa, jimilar mutane dubu 531 ne rikici ya tilasta masu barin matsugunansu tun daga watan Junairun 2012.

Matsala ta 'yan gudun hijira a kasar Mali ta samu asali ne daga rikicin 'yan tawaye masu dauke da makamai da ya barke a arewacin kasar, al'amarin da ya kai ga juyin mulkin a shekarar 2012 da kuma rikicin kabilanci a shekarar 2016. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China