in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Mali ya nada sabon firaministan kasar
2017-04-09 13:23:51 cri
A daren ranar 8 ga wata, gidan telebijin na kasar Mali ya sanar da cewa shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita, ya nada Abdoulaye Idrissa Maiga, a matsayin sabon firaministan kasar inda zai maye gurbin Modibo Keita da ya yi murabus a ranar 7 ga wata.

An haifi Maiga a birnin Gao dake arewacin kasar Mali a shekarar 1958, ya fara zama ministan tsaron kasar Mali tun daga watan Satumba na shekarar 2016, kana ya zama mataimakin shugaban Jam'iyyar kawancen kasar Mali dake kan karagar mulkin kasar.

Ana fuskantar barazanar tsaro a kasar Mali, tun daga ranar 9 ga watan Maris, likitoci da malaman makarantu sun shiga yajin aiki. Kuma Modibo Keita ya yi murabus a ranar 7 ga wannan wata.

Ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Mali ba ta bayyana dalilin da ya sa Modibo Keita ya yi murabus din ba, kana ba ta bayyana yaushe za a kafa sabuwar gwamnatin kasar ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China