in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Aljeriya da Mali sun tattaunawa game da harkar tsaro
2017-02-14 10:54:58 cri
Kasashen Mali da Aljeriya sun bayyana kudurinsu na karfafa hadin gwiwa ta fuskar tsaro a tsakaninsu.

Ministan kula da harkokin tsaro na kasar Mali Salif Traore wanda a halin yanzu ya ke ziyara a kasar Aljeriya shi ne ya bayyna haka, yana mai cewa, wannan ziyara wata dama ce ta kara bunkasa hadin gwiwa tsakanin dakarun kasashen biyu.

Ya kuma shaidawa manema labarai bayan ganawarsa da takwaransa na kasar Aljeriya Ramtane Lamamra cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu ta taimakawa dakarun tsaron kasarsa tun farkon shekarun 1960.

Jami'an biyun sun kuma tattauna batutuwa da dama, ciki har da hadin gwiwar tsaro da makatan yadda za su inganta yankunan dake kan iyakokin kasashen, da kuma aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar Mali.

Kasashen biyu dai suna kara daukar matakai don yakar kungiyoyin 'yan ta'adda a kan iyakokinsu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China