Gwamnatin kasar Mali ta bayar da sanarwa a wannan rana cewa, an shiga halin dokar-ta-baci a wannan karo don tinkarar barazanar ta'addanci, ta sanar da shiga halin dokar-ta-baci tun daga ranar 31 ga wannan wata na shekarar 2017 a kasar Mali na tsawon kwanaki 10.
Sanarwar ta bayyana cewa, idan ba'a samu kyautatuwa ba, bayan da aka yi bincike kan halin tsaro na kasar Mali, gwamnatin kasar za ta tsawaita wa'adin halin dokar-ta-baci.
Sanarwar ta kara da cewa, za a amince da hukumomin da abin ya shafa da su magance ta'addanci da barazanar da ake yiwa tsaron jama'a da dukiyarsu yayin da aka shiga halin dokar-ta-baci.
A ranar 20 ga watan Yuli na shekarar 2016, kasar Mali ta sanar da kafa dokar-ta-baci har na tsawon kwanaki 10 tun daga ranar 21 ga wannan wata. Daga baya, an tsawaita wa'adin zuwa ranar 29 ga watan Maris na shekarar 2017. (Zainab)