Wang Yi ya bayyana cewa, dalilin da ya sa Sin ta nuna goyon baya ga gudanar da dandalin shi ne, bukatar da ake da ita, ta koyi daga fasahohin tarihi da al'adun gargajiya, yayin da ake fuskantar yanayi mai sauyawa a duniya. Ya ce, a wannan karo, an gudanar da dandalin tare, wanda hakan ya ba da damar cimma daidaito a wadannan muhimman fannoni uku.
Da farko dai akwai batun wanzar da zaman lafiya. Domin shimfida zaman lafiya shi ne kan gaba ka rayuwar dan Adam, don haka ya kamata a warware rikice-rikicen duniya, da na yankuna cikin lumana, a kuma kaucewa amfani da karfin tuwo da yake-yake.
Na biyu kuwa shi ne fahimta juna. Inda ya ce, kamata a nuna daidaito ga daukacin al'adu, da fahimtar juna da koyi da juna, wanda ta haka ne za a samu ci gaba tare.
Na uku kuwa akwai batun hadin gwiwa. Ya ce, kamata ya yi a yi kokari tare, wajen kara hadin gwiwa don samun moriyar juna da wadata tare.(Zainab)