A jiya Alhamis 21 ga watan nan ne kwamitin sulhu na MDD ya kira babban taro game da batun kasar Sham, bisa shawarar da kasar New Zealand ta gabatar, a matsayinta na kasar da ke shugabantar kwamitin a wannan wata, taron da kuma ya samu halartar ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi.
A jawabin da ya gabatar yayin zaman, Mr. Wang Yi ya ce ya kamata bangarorin da abin ya shafa, su nace ga warware batun Sham daga tushe kuma ta hanyar siyasa, tare da kulawa da ra'ayoyin bangarori da dama.
Bugu da kari, Wang Yi ya jaddada cewa, ya kamata a aiwatar da kudurorin kwamitin na sulhu masu nasaba da batun Sham, musamman ma kuduri mai lamba 2254, a kokarin kyautata halin da Sham ke ciki a wannan shekarar da muke ciki.
Ya ce a matsayinta na mamba ta dindindin a kwamitin na sulhu, kasar Sin za ta ci gaba da sauke nauyin da ke wuyanta, na taka rawar gani a fannin cimma burin wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya. (Kande Gao)