Yayin ganawarsu, Wang Yi ya yabawa mista Ayrault kan yadda ya bayyana a fili cewa, ya na goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya, inda ministan na kasar Sin ya ce huldar dake tsakanin kasarsa da Faransa na cikin kyakkyawan yanayi.
A bana ne firaministan kasar Faransa zai kai ziyara kasar Sin, al'amarin dake nuna irin dangantaka ta kut-da-kut dake tsakanin bangarorin biyu.
Wang Yi, ya ce kasar Sin za ta yi kokari tare da kasar Faransa, don tabbatar da ganin ziyarar firaministan ta samu nasara, ta yadda za a samu damar bayyana hadin gwiwar kasar Sin da Faransa, gami da nahiyar Turai, a manyan tsare-tsare daban daban, don tunkarar yanayin koma-bayan tattalin arzikin duniya.
Haka zalika, ministan kasar Sin ya nanata cewa, kasarsa ta na goyon bayan yunkurin dinkewar kasashen Turai, kuma ta na son yin kokari tare da hadin gwiwar nahiyar Turai wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya.
A nasa bangare, minista Ayrault na kasar Faransa, ya ce bisa matsayinsu na kasashe masu kujerun din-din-din a kwamitin sulhu na MDD, kamata ya yi su kara kaimi don kare 'yancin sauran sassan duniya, maimakon kyale kasa daya ta yi babakere.(Bello Wang)