Merkel ta bayyana cewa, ta nuna goyon baya ga kiran "ziri daya da hanya daya" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, za ta tura ministan tattalin arziki da makamashi na kasar zuwa kasar Sin don halartar dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa kan "ziri daya da hanya daya", kana tana fatan za a gudanar da dandalin tattaunawar cikin nasara. Kasar Jamus tana shirya taron koli na Hamburg na kungiyar G20, ta yi imani da cewa za a samu kyakkyawan sakamako bisa goyon bayan kasar Sin a gun taron.
A nasa bangare, Wang Yi yana maraba da kasar Jamus ta tura babban wakilin kasar zuwa kasar Sin don halartar dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa kan "ziri daya da hanya daya". Ya bayyana cewa, a matsayin kasa ta shugabancin kungiyar G20 a karon da ya gabata, Sin tana son ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Jamus wajen gudanar da taron koli na Hamburg na kungiyar G20. (Zainab Zhang)