in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin shugabannin Sin da Faransa
2016-09-06 10:22:17 cri
A jiya Litinin 5 ga watan nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Faransa François Hollande, wanda ke halartar taron koli na G20 a nan kasar Sin.

Yayin ganawar tasu, Mista Xi ya bayyana cewa, taron G20 ya samu ci gaba mai armashi. Kaza lika Sin ta darajanta taimakon da Faransa ke ba ta. Ya ce, duk da irin canjin yanayin duniya, Sin na tsayawa tsayin daka wajen mai da Faransa matsayin abokiyarta mai muhimmanci a fannin hadin gwiwa, kuma za ta ci gaba da maida hankali kwarai game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a nan gaba.

A nasa bangare kuwa François Hollande ya taya wa kasar Sin na samun nasarar shirya taron koli na G20 a bangarori daban-daban, musamman ma ganin yadda aka amince da matsaya daya a fannin raya tattalin arziki, da cinikayyar duniya, da kuma tinkarar matsalar sauyin yanayi da dai sauransu.

Mr. Hollande ya kara da cewa, Faransa na dora matukar muhimmanci kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, ya kuma yi fatan kara tuntubar juna da yin mu'ammala, tare kuma da ci gaba da ciyar da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu gaba a fannoni daban-daban, ciki hadda harkar noma, da abinci, da samar da wutar lantarki ta karfin nukiliya. Sauran sun hada da yawon shakatawa, da raya muhalli, da wasu manyan batutuwan dake jawo hankali kasa da kasa da ma shiyya-shiyya. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China