Alkaluman da OECD ta gabatar sun nuna cewa, kasashen Sin da Afirka ta Kudu sun kasance a sahun gaba wajen samun saurin ci gaba. Alkaluman sun kuma nuna cewa, idan an kwatanta da alkaluman rubu'in farko na shekarar bana, saurin ci gaban tattalin arzikin Sin ya karu daga kashi 1.2% zuwa 1.8%, yayin da na kasar Afirka ta Kudu ya karu daga kasa da 0.3% zuwa 0.8%.
Sa'an nan idan an kwatanta da makamancin lokacin na shekarar bara, karuwar tattalin arzikin kasashen G20 a rubu'i na 2 ta kai kaso 2.9%, sa'an nan tattalin arzikin da ya fi saurin karuwa a lokacin shi ne na kasar Indiya da na kasar Sin.(Bello Wang)