in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana sa ran hadin gwiwar Sin da Amurka za ta ciyar da taron kolin G20 na Hangzhou gaba
2016-08-21 13:18:29 cri
Jakadan kasar Sin dake kasar Amurka Cui Tiankai ya bayyana a ranar 20 ga wata cewa, tun kafa tsarin kungiyar G20 ya zuwa yanzu, kasar Sin da kasar Amurka sun sha daidaita hadin gwiwar dake tsakaninsu, ana kuma sa ran kasashen biyu za su ci gaba da ba da gudummawa yadda ya kamata domin samun sakamako masu gamsarwa a yayin taron kolin kungiyar G20 da za a yi a birnin Hangzhou na kasar Sin a wata mai zuwa.

Haka kuma, Mr.Cui ya ce, ya kamata kasar Sin da Amurka su kara taimakawa wajen ciyar da taron kolin kungiyar G20 gaba, sabo da wannan shi ne nauyin da ya kamata kasashen biyu su dauka, kuma su cigaba da yin shawarwari kan wannan batu, don samun sakamako mai yawa.

A yayin taron kolin G20 da za a yi, shugabannin kasashen biyu za su yi wata ganawa, wadda duniya ke maida hankali kware da gasake kan ganawar da za su yi.

Dangane da wanann lamari, Mr. Cui ya bayyana cewa, ana fatan ganawar shugabannin kasashen biyu za ta kara karfafa fahimtar juna a tsakaninsu, ta kuma samar da hanyoyin karfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da Amurka, kana za ta taimaka wajen warware sabanin dake tsakanin kasashen biyu ta hanyar siyasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China