Wannan, shi ne karon farko da Mr. Guterres ya gana da shugaban na Amurka tun bayan ya kama aiki a matsayin babban magatakardan MDD a ranar 1 ga watan Janairun bana.
Stephane Dujarric ya bayyana cewa, a yayin ganawar, shugabannin biyu, wato Mr. Guterres da Mr. Trump sun tattauna kan yadda za a raya hadin gwiwar dake tsakanin MDD da Amurka a nan gaba. Sannan, sun cimma matsayar cewa, za su kuma ganawa a nan gaba kadan.
Rahotannin na cewa, ganawar shugabannin biyu ta shafe tsawon mintuna 15 zuwa 20.
Kakakin na MDD ya ce Antonio Guterres wanda kafin ganawarsa da shugaban na Amurka, ya gana da mataimakinsa kan harkokin tsaron kasa Mike Master, ya yi murna sosai da samun damar tattaunawa da Shugaba Donald Trump.
Har ila yau, Mr. Dujarric ya ce a halin yanzu, babban magatakardan na halartar taron yanayin bazara tsakanin Asusun ba da lamuni na duniya IMF da bankin duniya a birnin Washington na Amurka. (Maryam)