Cikin sanarwar, MDD ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, ta kuma yi fatan samun waraka cikin hanzari ga wadanda suka jikkata.
An gudanar da aikin kwashe mutanen ne bisa yarjejeniyar da aka kulla, shi ya sa, MDD ta yi kira ga bangarori daban daban da su tabbatar da tsaron mutanen da aka kwashe su daga yankin dake fama da hare-haren.
Haka zalika, wani jami'in gwamnatin kasar Syria ya bayyana a jiya cewa, an kai harin kunar bakin wake ga motoci da dama dake dauke da mabiya mazahabar Shia a yammacin birnin Aleppo na kasar, wadanda aka janye su daga yanki mai fama da hare-hare, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla guda 70, yayin da 128 suka jikkata. (Maryam)