Cikin mambobin kwamitin 15, 10 sun amince da kudurin, inda kasashen Bolivia da Rasha mai kujerar naki suka ki amincewa, yayin da kasashen Sin da Habasha da Kazakhstan suka kauracewa kada kuri'ar.
Kudurin da Birtaniya da Faransa da Amurka suka gabatar, na neman rundunar sojin Syria ta ba masu bincike na MDD damar samun cikakkun bayanai kan ayyukanta a ranar da aka kai harin da ake zargi.
Kudurin ya kuma yi tir da amfani da makamai masu guba, tare da neman awaitar da bincike kan batun cikin gaggawa.
Wakilin kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya ce kasar na goyon bayan MDD da hukumar haramta amfani da makamai masu guba (OPCW) wajen aiwatar da binciken tsanaki mai ma'ana ba tare da nuna fifiko ga wani bangare ba.
Har ila yau, Liu Jieyi ya ce kasar Sin na goyon bayan kunshin kudurin da ya yi tir da amfani da makamai masu guba da kuma neman gudanar da bincike kan harin da ake zargi.
Sai dai, ya ce kasar Sin ta kauracewa kada kuri'ar ne saboda akwai bukatar yiwa wasu sassansa gyara, domin cimma matsaya guda tsakanin mambobin kwamitin. (Fa'iza Mustapha)