in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira da a samar da yanayin magance rikice-rikice a duniya
2017-04-19 13:53:46 cri
Zaunannen wakilin Sin dake MDD Liu Jieyi,ya ce manufar magance rikice-rikice ita ce, kafa duniya mai zaman lafiya, yana mai kira da a samar da hanyoyin magance rikice-rikice da ake fuskanta a duniya.

Liu Jieyi ya yi wannan jawabi ne a jiya, yayin taron kwamitin sulhu na MDD kan kula da hakkin dan Adam da magance rikice-rikice, inda ya ce, alhakin magancewa da warware matsalolin barkewar rikice-rikice ya rataya ne a wuyan kwamitin sulhu bisa tsarin mulkin MDD.

Har ila yau, wakilin na kasar Sin, ya yi kira da a warware matsalolin dake tsakanin kasa da kasa ta hanyar hawa teburin sulhu, da mai da hankali ga musababbin aukuwar rikici, da yin amfani da muhimmiyar rawar da kungiyoyin yankuna ke takawa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China