Yayin taron manema labarai na kulla yaumin a jiya, Stephane Dujarric, ya ce Nana Akufo Addo zai shugabanci shirin ne tare da Firayministan kasar Norway Erna Solberg har zuwa karshen shekarar 2018.
Shirin muradun ci gaba masu dorewa da aka kaddamar a ranar 21 ga watan Janairun bara, ya kunshi fitattun mutane 17 a matsayin wakilai da za su taimakawa Sakatare Janar na MDD tabbatar da cimma manufofin shirin, da shugabannin kasashen duniya baki daya suka amince da shi a watan Satumban 2015.
Tun bayan da ya kama aiki ranar 1 ga watan Janairu, Sakatarre Janar na Majalisar Antonio Guterres ya sanya cimma muradun a cikin jerin batutuwan da ya fi ba muhimmanci, wanda ke da manufar samar da ci gaba a duniya nan zuwa shekarar 2030. ( Fa'iza Mustapha)