Wata sanarwa da kwamitin mai mambobin kasashe 15 ya rabawa manema labarai, ya bukaci kasar Koriya ta Arewan da ta hanzarta dakatar da duk wani shiri da zai keta kudurin kwamitin sulhun. Kwamitin sulhun ya ce zai ci gaba da sanya ido kan yanayin da ake ciki kuma zai dauki matakan da suka wajaba ciki har da sanya mata takunkumi.
Kwamitin sulhun ya kuma bayyana rashin jin dadinsa game da kunnon kashin da kasar take nunawa da kuma yadda take takalar kwamitin sulhun ta hanyar harba makamai masu linzami.
Rundunar sojojin kasar Koriya ta Arewa ta sanar da cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ce kasar Koriyar ta Arewan ta yi gwajin wani makami mai linzami da ba a bayyana sunansa ba a gabar tekun gabashin kasar. Sai dai daga bisani kasar Amurka ta tabbatar da cewa, gwajin bai yi nasara ba.(Ibrahim)