Cikin wata sanarwar da aka gabatar daga birnin Kampala na kasar Uganda, shugaba Museveni da Mista Ban sun ce, shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar sun gaza mutunta cikakken goyon bayan da bangarorin kasa da kasa suke nunawa wannan jaririyar kasa.
Museveni ya ambaci abubuwa 3 masu mumimmanci da ya kamata a lura da su a halin yanzu, da suka hada da kafa wata rundunar kiyaye zaman lafiya a yanki, da tsagaita bude wuta a Juba, gami da kaddamar da babban zabe da maido da tsarin dimokuradiya a kasar cikin gaggawa.
A nasa bangaren, Ban ya ce yadda shugabannin 2 na Sudan ta Kudun suka yi watsi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, ya sa MDD cikin wani mawuyacin hali, don haka ya yi kira ga shugaba Museveni, wanda shine mai shiga tsakani, da ya yi kokari tare da kungiyar AU da sauran bangarorin yankin don nuna kin amincewa da sake barkewar yaki a kasar a nan gaba.(Bello Wang)