Jiya Alhamis ne mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya ce kamata ya yi aikin wanzar da zaman lafiya ya taka rawa a shiyya-shiyya, kuma a hade shi da aikin kandagarkin abkuwar tashe tashen hankula.
An dai gudanar da babban taron MDD karo na 71, inda aka nazarci rahoton kwamitin shimfida zaman lafiya da kuma asusun shimfida zaman lafiya na MDD. A yayin taron ne kuma Wu Haitao, ya ce yanzu haka dukkan kasashen da ke cikin ajandar kwamitin shimfida zaman lafiya, kasashe ne na nahiyar Afirka. Don haka kamata ya yi MDD da kasashen duniya, su mara wa kungiyar Tarayyar Afirka baya, wajen aiwatar da taswirar tsarin shimfida zaman lafiya da tsaro tsakanin shekarar 2016 zuwa ta 2020, da ma sauran shirye-shirye, a kokarin taimakawa kasashen nahiyar samun dauwamammen zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da wadata. (Tasallah Yuan)