Nicholas Rosellini, jami'in MDD game da kasar Sin, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar jarin da kasar Sin ke zubawa a fannin makamashi, musamman ta hanyar samar da makamashi marar gurbata muhalli zai taimakawa nahiyar wajen samar da guraben ayyukan yi masu yawan gaske.
A bisa kididdiga, mutane miliyan 600 ne basu da hasken lantarki a Afrika.
Nicholas ya yabawa kasar Sin sabo da tallafawa kasashen Afrika da dama wajen samar da makamashi marar gurbata muhalli, ya ce baya ga rawar da Sin ke takawa wajen bunkasa cigaban tattalin arzikin nahiyar ta Afrika, hasken lantarki wani muhimmin jigo ne da ya shafi bukatu na rayuwar bil adama.
Jami'in ya bada tabbacin marawa kasar Sin baya karkashin shirin raya cigaban kasashen duniya na MDD wato UNDP domin ta samu zarafin aiwatar da shirye shirye da suka shafi cigaban nahiyar ta Afrika, musamman shirye shiryen da za su samarwa Afrikan cigaba mai dorewa.(Ahmad Fagam)