A gun taron, an ce, bayan da aka samu nasarar aikin bisa mataki na farko, gwamnatin kasar Sin ta kara samar da kudi dala miliyan 4 don tsawaita wa'adin gudanar da aikin da shekaru biyu. Kuma za a shigar da kasashen Togo da Zambia a cikin jerin kasashen da za a gudanar da aikin bisa mataki na biyu, don haka yawan kasashen da za su samu moriya daga aikin ya karu zuwa 10 a Afirka.
Babban direkta a fannin ba da ilmi na kungiyar UNESCO Tang Qian, ya yi jawabin bude taron, inda ya bayyana cewa, an samu nasarori wajen gudanar da aikin bisa mataki na farko. Aikin ya sa kaimi ga cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa na MDD, musamman a fannonin ba da ilmi mai inganci da samar da damar yin karatu ga dukkan jama'a.
Zaunannen wakilin Sin dake kungiyar UNESCO Shen Yang, ya yi nuni da cewa, Sin za ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwarta tare da kungiyar UNESCO don sa kaimi ga cimma ajandar samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030, musamman wajen samun zaman lafiya da 'yancin kai da bunkasuwa mai dorewa a nahiyar Afirka. (Zainab)