Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a yau Jumma'a a nan Beijing cewa, kamata ya yi shugaban majalisar Turai mista Antonio Tajani, ya bayyana ra'ayinsa game da alakar Sin da nahiyar Afirka, bayan ya samu cikakkiyar masaniya game da hakan.
Kalaman na Mr. Lu na zuwa ne bayan da Mr. Tajani ya bayyana cewa, a ganin sa mai yiwuwa ne kasar Sin, na shirin yi wa nahiyar Afirka mulkin mallaka. Mr. Lu Kang ya maida martini yayin da yake amsa tambayar manema labaru, a gun taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, inda ya ce, idan ba a manta ba, kasashen Turai ne suka yiwa Afirka mulkin mallaka a duk sassan duniya can a baya. Ya ce kuma tun ba yau ba kasar Sin ke tallafawa kasashen Afirka, tare da zuba jari, da yin hadin gwiwa tare da kasashen nahiyar.
Kaza lika Sin ta fara taimakawa 'yan uwanta na Afirka ne bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, a kuma daidai lokacin da ita ma Sin take matsayi na baya a ci gaba tana kuma fama da kangin talauci.
Don haka dai a cewar Mr. Lu, kasar Sin tana mara wa Afirka baya ne, a kokarin ganin kasashen nahiyar sun samu 'yancin kai ta fuskar siyasa, tare da tsayawa kan kafafunsu. Yayin da a hannu guda jama'ar nahiyar ke matukar maraba da wannan mataki. (Tasallah Yuan)