Yau Jumma'a ne ministan harkokin wajen kasar Eritrea Osman Saleh, ya ce yana fatan kasashen Afirka za su jure wahalar da suke fuskanta, su kuma warware matsalolinsu a gida. Kaza lika su hada kai da kasar Sin wajen aiwatar da shirin aiki da aka amincewa na taron Johannesburg, karkashin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, a kokarin kara kawo wa jama'ar Afirka alherai.
Osman Saleh ya fadi hakan ne yayin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua a wannan rana.
Osman Saleh dai ya shafe kwanaki 6 yana ziyarar aiki a nan kasar Sin, bisa gayyatar da takwaransa na kasar Sin Wang Yi ya yi masa. (Tasallah Yuan)