Shugabar Kungiyar Red Cross a nahiyar Afrika Patricia Danzi wadda ta bayyana hakan, ta ce manufar ziyarar da ta yi niyyar kai wa Beijing cikin wannan wata ita ce, neman kara karfafa hadin gwiwa domin magance matsalar agajin jin kai da ake fuskanta a Afrika.
Da take ganawa da manema labarai a birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu Patricia Danzi ta ce janyo hankalin Sinawa game da halin da ake ciki na da matukar muhimmanci saboda abu mafi wahala shi ne kawar da matsalolin.
Ta kara da yin kira ga masu bada gudunmowa, su gaggauta bayar da tallafi domin kare kara ta'zzarar al'amura a kasar Sudan ta Kudu da MDD ta ayyana matsalar yunwa a wasu sassan kasar, inda mutane 100,000 ke fuskanatar yunwa yayin da wasu miliyan daya ke gab da fuskantar yunwar.
Har ila yau, ta ce fada, da gudun hijira da rashin abinci mai gina jiki sun jefa lafiyar mutane cikin mawuyacin hali, ta na mai cewa, fari da rikice-rikice ya kara jefa al'ummomin kasashen Sudan ta Kudu da Somaliya cikin matsanancin hali. (Fa'iza Mustapha)